DAGA JOHN D. WADA, a LAFIYA
Babban daraktan gidauniya Cleft & Facial Deformity Foundation, Dokta Saidu Bello, ya ce kawo yanzu gidauniyar ta yi wa masu fama da cutar kumburin fuska su sama da 4000 tiyata kyauta.
Ya ce waɗanda suka ci gajiyar wannan shiri an zaɓo su ne daga sassan ƙasa, kuma an yi aikin cikin nasara batare da fuskantar wata matsala ba.
Bello ne ya sanar da haka ne a jawabin sa a wajen taron ƙaddamar da ci gaba da aiwatar da shirin a jihar Nasarawa wanda aka gudanar a asibitin tarayya, wato Federal Medical Centre, da ke garin Keffi a ranar Talata.
A cewar Bello, an kafa gidauniyar ce da nufin agaza wa masu fama da cutar kumburin fuska, musamman marasa galihu a cikin al’umma. Cutar da a cewarsa, har yanzu ba a gano musabbabin da ke haifar da ita ba.
Ya ƙara da cewa, da farko an tsara shirin ne don yi wa kimanin mutum 50 aiki jihar Nasarawa amma daga bisani ya kasance aka samu masu ɗauke da cutar fiye da hakan.
Daga nan, Likitan ya yi amfani da dama wajen jinjina wa Gidauniyar T.Y Danjuma dangane da gudumawa da tallafin da ta dade tana bai wa gidauniyar musamman ɗaukar nauyin shirye-shiryenta.
Da yake tofa albarkacin bakinsa, Shugaban FMC Keffi, Dokta Yahaya Adamu da shugaban fannin kula da hakori da wakilin gidauniyar taimako ta T.Y. Danjuma da sauran manyan baƙi da suka yi jawabi a wajen taron ƙaddamar da shirin, duk sun yaba wa ƙoƙari da hangen nesan gidauniyar CFDF na samar da agajin kiwon lafiya ga marasa galihu cikin al’umma.
