An kama ɗan shekara 80 da yin lalata da ‘yar shekara 10 a Bayelsa

Spread the love

‘Ƴan sanda a Jihar Bayelsa sun yi nasarar cafke wani dattijo mai shekaru 80 da zargin yin lalata da yar shekara 10.

Lamarin ya faru a Otuakpoti dake ƙaramar hukumar Ogbia a Jihar Bayelsa.

Mai magana da yawun yan sanda na Jihar, ASP Musa Muhammad ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace tuni an miƙa lamarin sashen binciken manyan laifuka domin cigaba da bincike.

Bayanai sun nuna cewa, dattijon ya jima yana lalata da yarinyar har tsawon wata 12 kafin dubun shi ta cika.

An sami nasarar cafke tsohon ne da taimakon wata ƙungiya mai rajin kare haƙƙin mata.

By ukarofi