
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Hukumar zaɓe ta jihar Kogi ta ayyana 19 ga watan Oktoban shekarar nan a matsayin ranar da za ta gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a faɗin jihar.
Hukumar ta yi sanarwar ne yayin da ake ganin hakan bai rasa nasaba da hukuncin kotun ƙoli na ranar 11 ga watan Yuli kan zartar da cin gashin kai ga ƙananan hukumomi.
Kotun ƙolin ta ce daga ranar da ta yi hukuncin, dukkan ƙananan hukumomi za su koma karɓar kasafinsu daga ofishin Akanta Janar na ƙasa ba tare da wani shamaki ba, sannan kuma ta bayyana rashin halascin kwamitin riƙon ƙwarya ga kundin dokar ƙasa.
A ranar 5 ga watan Yuli, 2024 ne Majalisar dokokin jihar ta ƙara wa’adin miƙa mulki ga kwamitin shugabannin ƙananan hukumomi da watanni shida-shida a yayin wani zama da ta yi, bayan da gwamnan jihar, Usman Dodo ya aika wa Majalisar wata takarda da ke da alaƙa da hukuncin.
A lokacin da yake miƙa jadawalin lokacin zaɓen ga masu-ruwa-da-tsaki, Mamman Nda-Eri domin amincewa, ya bada tabbaci ga dukkan jam’iyyun siyasa a jihar cewa sun shirya zaɓen ne ta hanyar bai wa kowace jam’iyya damar a dama da ita da yin komai a idon jama’a tare da kiyaye doka da oda.
Nda-Eri ya ƙara da cewa, sun shirya yin zaɓen bisa ga adalci tare da bin doka da oda domin tabbatar da gaskiya a cikinsa.
Kazalika, shugaban hukumar zaɓen ya nemi masu-ruwa-da-tsaki da su cigaba da basu goyon baya tare da kira ga jam’iyyu da su kiyaye dokokin zaɓen.
