Gwamna Abba Kabir Yusuf ya Sama Dokar kafa sababbin masarautu uku a Jihar Kano hannu

Spread the love

Daga RABIU SANUSI

Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya sakama sabuwar dokar samar da sababbin masarautu uku hannu ta sarakuna masu daraja ta biyu, dan bunƙasa harkokin cigaba da zaman lafiya.

Gwamnan yayin da yake sa ma dokar hannu ya bayyana cewa ƙirkiro wannan sabbin masarautu guda uku zasu taimaka matuka wajen samar da zaman lafiya da cigaba tare da bunƙasa al’adun wannan jiha mai albarka.

Haka kuma gwamna Abba Kabir yace duba da yadda masarautun gargajiya ke taimakawa matuƙa yasa dole aduba yadda za’a ƙara inganta hanyoyin cigaba a wannan jiha ta Kano ta hanyar masarautu.

“Wannan yunƙurin zai tamaikama musamman al’ummar dake wannan yanki guda (ukku) ta fuskar tattalin arziki, tsaro da zaman lafiya dan ganin mahimmancin su.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma ce a yau wannan rana tana da mahimmanci a tarihin jihar Kano da bazai taba gogewa ba ta yunkuri da majalisar dokokin jihar tayi na zama na farko har na uku dan tabbatar da kafuwar wannan masarautu masu daraja ta biyu.

Masarautun da gwamnan ya bayyana an samar sun haɗar da GAYA,AJINGI, ALBASU, sai RANO, KIBIYA,BUNKURE da kuma masarautar KARAYE,ROGO.

“Dan haka muke kira ga Al’ummar wannan jiha mai Albarka dasu cigaba da bamu haɗin kai da goyon baya dan samun ƙwarin gwuiwar gudanar da aiki dan taimakon jihar mu mai albarka.

Gwamna ya kuma bayyana cewa nan bada jimawaba zasu bayyana sarakunan da zasu jagoranci wannan masarautu masu daraja ta biyu.

By ukarofi