Matatar Ɗangote ta kuka da ƙarancin ɗanyen mai

Spread the love

Matatar Ɗangote ta kuka da ƙarancin ɗanyen mai

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Kula da Masana’antun Dangote ta dage cewa har yanzu kamfanonin mai na ƙasa da ƙasa suna cike da takaicin yadda ake samar da ɗanyen mai ga matatar ta mai ɗaukar nauyin fitar da gangan 650,000 a kowace.

Kamfanin ya bayyana hakan ne a daidai lokacin da ta yaba wa Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya bisa irin ayyukan da ta ke yi a kan buƙatun da kamfanin mai ke yi na samar da ɗanyen mai daga IOC, da kuma ƙa’idojin samar da ɗanyen mai a cikin gida don tabbatar da gaskiya a harkar man fetur.

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Larabar da ta gabata, kamfanin Dangote ya yi zargin cewa IOC sun dage kan sayar da ɗanyen man fetur ga matatar ta ta hannun wakilansu na ƙasashen waje, inda ta ce farashin ɗanyen mai a cikin gida zai ci gaba da ƙaruwa saboda cinikin makamai na sayar da kaya akan dala 2 zuwa dala 4 kan kowacce ganga, sama da haka.

Kamfanin ya kuma yi zargin cewa kamfanonin da ke haƙo mai na aasashen waje suna ganin sun fi baiwa ƙasashen Asiya fifiko wajen sayar da ɗanyen da suke haƙowa a Nijeriya.

Mataimakin shugaban kamfanin nai da iskar gasa na Ɗangote, Mista DVG Edwin, ya ce, “Idan aka aiwatar da aa’idojin samar da ɗanyen mai a cikin gida da kyau, hakan zai tabbatar da cewa mun yi hulɗa kai tsaye da kamfanonin da ke haƙo ɗanyen mai a Nijeriya kamar yadda hukumar ta tsara a Dokar Masana’antar Man Fetur.”

Edwin ya dage cewa IOCs da ke aiki a Nijeriya sun ci gaba da daƙile buƙatun kamfanin na ɗanyen da ake samarwa a cikin gida a matsayin kayan abinci don aikin tace shi.

Ya bayyana cewa, idan aka ba wa kamfanin man kayayyaki, wani lokacin yana kan farashin dala 2 zuwa dala 4 (kowace ganga) sama da farashin da hukumar NUPRC ta ƙayyade.

By ukarofi