Turkiya ta amince da tura dakarunta zuwa Somaliya da yaƙi ya ɗaiɗaita

Spread the love

Wannan shiri an yi shi ne da nufin tallafa wa ayyukan yaƙi da ta’addanci a birnin Mogadishu, kuma ya zo ne watanni bayan da ƙasashen biyu suka rattaba hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwa ta tsaro da kuma tattalin arziki.

Al-Shabab mai alaƙa da ƙungiyar Al Ƙaeda ta dade tana fafatawa da gwamnatin Somalia a ƙoƙarin da ta keyi na kafa Ƙasar islama tun a shekara 2006.

Turkiyya ta shafe sama da shekaru goma, tana taimaka wa somalia wajen horas da sojojin ƙasar, da bata taimako ta ɓangarori daban daban don habbaka tsarin tabbatar da tsaro da zaman lafiya.

Sai dai jami’an Turkiyya sun ce ƙalubalen tattalin arziki ya hana sojojin Somaliya yin cikakken tasiri wanda ake ganin ɗaukin da Turkiyya ta bata zai taimaka wajen samun salama.

By ukarofi