‘Yan takara su 97 ne ke shirin shiga a fafata da su a zaɓen da ke cigaba da shan suka.
Tunisiya ta fara karɓar takardun neman tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasar da za a gudanar a ranar 6 ga watan Oktoba mai zuwa, a daidai lokacin da masana ke cewa akwai gagarumin tazgaro ga masu ƙalubalantar shugaba mai ci Kais Saied.
An dai sauya sharuɗɗan da ake so mutum ya cika domin tsayawa takara, a ƙarƙashin jagorancin Saied, mai shekaru 66, wanda aka zaɓa a shekarar 2019.
Idan ba a manta ba, da dama daga cikin masu son tsayawa takara, ba za su samu ko da fom ɗin nuna sha’awar tsayawa takarar farko ba, sakamakon suna gidan yari.
