WAEC ta riƙe sakamakon jarrabawar ɗalibai 215,267 bisa satar amsa

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Sakandire ta Afrika ta Yamma, WAEC, ta dakatar da sakamakon jarrabawar ɗalibai 215, 267, bisa zargin tafka maguɗi.

Amos Dangut, shugaban ofishin na ƙasa ne ya bayyana haka a lokacin da yake bayyana sakamakon a ranar Litinin, a Legas.

A cewar Dangut, adadin ya nuna kashi 11.92 na ɗaliban da suka zana jarrabawar.

Ya bayyna cewa adadin ya ragu da kashi 4.37 cikin ɗari idan aka kwatanta da kashi 16.29 da aka samu a bara, a cikin 2023.

“Sakamakon da aka hana na waɗannan ɗalibai da suka zana jarrabawar na da alaƙa da wasu rahotanni da aka bayar na rashin gudanar da jarrabawar cikin sahihanci.

“Yawancin amfani da wayar salula a ɗakin jarrabawar, duk da dokar hana maguɗi da shirya maguɗi a wasu makarantu, wasu batutuwa ne masu ban tsoro.

“Ana binciken dukkan lamuran kuma za a gabatar da rahoton binciken ga kwamitin da ya dace na majalisar, don nazari da yanke hukunci na karshe,” inji shi.

Shugaban na WAEC ya ƙara da cewa za a sanar da hukuncin kwamitin ga waɗanda abin ya shafa ta makarantunsu daban-daban, nan gaba kadan.

By ukarofi