Gwamnati na sa ran samar da ayyuka miliyan biyu daga Ma’aikatar Ƙirƙira

Spread the love

Ministar Ma’aikatar ƙirƙire ƙirƙire Hannatu Musawa ta bayyana wani shirin zuba hannu jari na biliyan 100 da samar da ayyuka miliyan biyu daga ma’aikatar ƙirƙire ƙirƙire.

Ministar ta bayyana haka ne a wata hira da tayi, inda ta faɗi cewa, gwamnati na shirin ganin cewa hannun jari da ake zubawa a fannin muma mun samu wani kaso daga wannan jarin.

Minista Musawa ta ci gaba da cewa, hakan zai iya faruwa ganin yadda gwamnati ke jajircewa da kuma irin damammaki da ke cikin masana’antar ƙirƙire-ƙirƙire.

Ta ƙara da cewa suna ƙoƙarin samun haɗin kai da ƙungiyoyi da masana’antu masu zaman kansu domin ganin wannan aikin ya samu nasara.

Daga ƙarshe ta bayyana cewa za su haɗa kai da Bigwin Philantrophy, domin taimakawa ma’aikatar wajen ganin an samu cigaban da ake buƙata ta fannin samar da ayyukan yi da sauran al’amuran cigaba.

Ta bayyana wannan haɗin kai a dalilin aikin da kamfanin yayi a ƙasar Rwanda ta hanyar taimakawa wajen samar da ayyuka 500,000 a ƙasar.

By ukarofi