Badaƙalar N90b: Tsohon shugaban NAHCON ya bar hannun EFCC

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Hukumar hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati, EFCC ta sako tsohon shugaban hukumar jigilar alhazai (NAHCON), Jalal Arabi da Sakatarensa Abdullahi Kontagora bayan belin su da aka yi.

An tsare su ne sakamakon zargin sarrafa Naira biliyan 90 kuɗin tallafi ga mahajjatan shekarar 2024 da gwamnati ta ware inda rashin cike sharuɗɗan sako su ya sanya suka kai kwana biyar a hannun EFCC.

Wata majiya ta ce an sako su ne a ranar Litinin Bayan cike ƙa’idodin beli da suka yi.

Sannan, ta kuma ce, baya ga gano Riyal 319,098 da aka yi, kawo yanzu ba a sake samun wasu adadin kuɗaɗen badaƙalar ba duk da cewa har yanzu ana cigaba da gudanar da bincike game da lamarin.

A lokacin haɗa wannan rahoton, an yi ƙoƙarin samun mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, amma ba a samu damar hakan ba kuma bai amsa saƙon da aka tura masa ba game da batun.

Rahoton binciken EFCC ya nuna yadda Arabi ya biya kansa da wasu muƙarrabansa sama da yadda doka ta amince mu su cikin Naira biliyan 90 da aka ware don tallafi ga mahajjatan 2024.

By Babaji