Jinkirin kai kuɗin fansa ya sa ƴan bindiga suka kashe mahaifina – Ɗan marigayi Sarkin Gobir

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Ɗaya daga cikin ƴaƴan marigayi Sarkin Gobir a ƙaramar hukumar Sabon Birni da aka kashe, Hon. Shuaibu Gwanda Gobir ya ce rashin kai kuɗin fansa wa ƴan bindiga daga gwamnatin jihar Sakkwato ya sa mahaifinsa ya rasa ransa.

Makonni uku da suka gabata ne ƴan ta’adda suka yi garkuwa da Sarkin mai suna Alhaji Isa Muhammad Bawa tare da ɗaya daga cikin ƴaƴansa inda suka buƙaci a bada miliyan N60 wanda a ciki suka ce a saya mu su babur guda biyar.

An kashe Sarkin ne a ranar Talata, 20 ga watan Agusta, kwana ɗaya bayan sako wani bidiyo da ƴan bindigar suka yi na dukan sa da su ke yi.

Bayan sako bidiyon ne sai Hon. Gwanda a wata hira da manema labarai ya ce sun yanke shawarar haɗa kuɗin a tsakaninsa da sauran mambobin ahalin gidan Sarkin, sai suka samu labarin cewa gwamnatin jihar ta ce za ta biya a ranar Litinin.

A ranar ne kuma suka ji labarin an fitar da kuɗin inda ya ce suka buƙaci gwamnatin ta kai ma ƴan bindigar tunda ta na tattaunawa da su.

Daga nan ne sai suka samu labarin Sarkin ya rasu a washe gari ba tare da samun rahoton kai kuɗin fansar ba.

By Babaji