Gwamnan Filato ya dakatar da kwamishinoni biyu da wasu hadimansa kan zargin fallasa sirri

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamna Caleb Mutfwang na Jihar Filato, ya dakatar da wasu kwamishinoni biyu masu ci da wasu hadimansa.

Mutfwang, ya sanar da dakatarwar ne a wata sanarwa da Mista Gyang Bere, daraktan yaɗa labaransa, ya fitar a ranar Talata a Jos.

Ya ce gwamnan ya amince da dakatar da jami’an, ba tare da karin bayani kan dalilan ɗaukar matakin ba.

Wata majiya da ke kusa da gwamnan ta shaida wa News Point Nigeria cewa an zargi kwamishinonin da aka dakatar da aika shirye-shiryen zaɓen ƙananan hukumomi zuwa ga ‘yan adawa a jihar kuma ana zargin mashawarcin na musamman da fallasa wasu bayanan gwamnati na sirri.

Jami’an da abin ya shafa sun haɗa da kwamishinan kasafin kuɗi da tsare-tsare na tattalin arziki, Chrysanthus Dawm da kwamishiniyar yawon buɗe ido, al’adu da karɓar baki, Jamila Tukur.

Sauran waɗanda abin ya shafa sun haɗa da mai ba da shawara na musamman kan raya karkara Dio Lamul da kuma jami’in hulɗa da jama’a na mazaɓar Mikang, Moses Sule.

A wani labarin kuma, Gwamnan ya kuma yi wani sauyi kaɗan a majalisar zartarwarsa tare da yin sauyin muƙamai a cikin mambobi biyu na majalisar zartarwarsa domin inganta hidima ga al’ummar jihar Filato.

A ƙarkashin sabon tsarin, Noel Nkup, kwamishinan albarkatun ruwa da makamashi na yanzu, zai zama kwamishinan matasa da ci gaban wasanni.

Hakazalika, Bashir Lawandi Datti, wanda a baya ya riƙe muƙamin Kwamishinan Matasa da Cigaban Wasanni, an mayar da shi Kwamishinan Albarkatun Ruwa da Makamashi.

Dakatar da jami’an dai bai rasa nasaba da zaɓen fidda gwani na jam’iyyar PDP na ƙananan hukumomi da aka gudanar a jihar wanda ya yi fama da tashe-tashen hankula a wasu ƙananan hukumomin da kuma ƙorafe-ƙorafen kutse a wasu yankunan.

By ukarofi