Gwamnatin Tarayya tare da ƙungiyar malaman jami’o’i na ƙasa sun sake ɗage zaman tattaunawa da su ka shirya yi har sai shida ga watan Satumba.
Wannan taron ya biyo bayan matsayar da Majalisar zartaswa ta ƙungiyar ta samu matsayar shiga yajin aiki domin nuna rashin jin dadi a kan gazawar gwamnati wajen aikata yarjejeniyar da ƙungiyar tayi tun shekarar 2009.
A cikin abinda ƙungiyar malaman ke nema akwai kula da walwalar malaman da kuma tsagaita ƙirƙirar sabbin jami’o’i a ƙasar har sai an gyara waɗanda ke akwai.
A cikin wani martani da Ministan ilmi na ƙasa Farfesa Mamman Tahir ya bayar ga buƙatun ƙungiyar ya bayyana cewa, waɗannan matsalolin tun 1981 da kuma matsalar cire malaman Jami’o’i daga tsarin biyan albashi na IPPIS wanda yace yanzu haka gwamnatin na kan aikin tabbatar da faruwar hakan.
Daga ƙarshe ministan ya buƙaci ƙungiyar su rungumi tattaunawar da niyya mai kyau domin samun mafita mai ɗorewa.
