Tajuddeen Dantata ya zama darakta a Bankin Jaiz

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Bankin Jaiz, shahararren bankin Musulunci a Nijeriya, ya sanar da naɗin Tijudeen Aminu Dantata a matsayin sabon Darakta da ba zartarwa ba.

A cikin wata sanarwa, bankin ya tabbatar da cewa babban bankin Nijeriya (CBN) ya amince da riƙon amanar Dantata. Babban bankin ya nuna cewa ƙwarewarsa a fannonin daban-daban zai ƙara inganta harkokin bankin.

“An naɗa Tajuddeen Aminu Dantata ne a matsayin babban daraktan da ba zartarwa ba a bankin Bankin Jaiz bayan amincewar bankin CBN”, inji sanarwar.

Dantata zai kawo ƙwarewarsa a muƙamin a  matsayi wanda ya yi aiki a kamfanoni da dama, kamar kamfanin man fetur da kuma gas na Dantata. Bugu da ƙari, ya yi aiki a matsayin darakta a Kamfanin Meter na Coɓerity na Nijeriya, Namco Nijeriya, da Bebela Nigeria Liɓed, da Bebeji.

“Ya shiga cikin shirye-shiryen horo daban-daban, a gida da na wajen Nijeriya. Yana da ƙwarewa. Bankin yana da yaƙinin cewa Alhaji Tajudeen zai ƙara haɓaka ayyukan bankin,” inji sanarwar.

By ukarofi