NYSC ta sanar da zaɓin canja wurin hidima ga matan aure

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Masu Yi Wa ƙasa Hidima ta Nijeriya, NYSC, ta buƙaci matan aure ’yan yi wa ƙasa hidima waɗanda aka tura jihohin da ba mazajensu da su nemi canjin wurin hidima.

Hukumar ta bayyana hakan ne a wani saƙon da ta wallafa a shafinta na ɗ a ranar Litinin.

Sanarwar ta ce, “ZUWA GA DUKKAN MATAN AURE A RUKUNIN BATCH “B” STREAM II.

“Dukkan matan da suka yi aure (PCM) da aka tura jihohin da ba mazajensu a can, su kai rahoto ga sansanin masu yi wa aasa hidima na NYSC mafi kusa domin a sauya musu jiharsu.

“Za su bayar da rahoto a lokacin rajista a sansanoni tare da kwafin shaidar aurensu da sauran takaddun da suka dace a matsayin shaida. Da zarar an yi canjin zai nuna a shafin bayanin su.”

NYSC shiri ne da gwamnatin Nijeriya ta kafa da nufin haɗa kan ɗaliban da suka kammala karatun digiri a fannin gina aasa da ci gaban ƙasa.

An kafa shi ne a ranar 22 ga Mayu, 1973, bisa ga doka mai lamba 24, wadda ta bayyana cewa, an ƙirƙiro shirin ne “da nufin samun kwarin gwiwa da bunƙasa alaaa tsakanin matasan Nijeriya da kuma inganta haɗin kan ƙasa”.

Don cancanta, masu digiri dole ne su kasance ƙasa da shekaru 30 bayan kammala karatun.

Waɗanda suka haura shekaru 30 suna samun takardar shaidar ficewa, kwatankwacin takardar sallamar NYSC.

By ukarofi