
Daga BELLO A. BABAJI
Ɗaruruwan ƴan adaidata sahu ne suka yi cincirindo a titunan cikin garin Kano a ranar Talata inda suke nuna rashin jin daɗinsu game tashin gwaoron zabi da farashin man fetur yayi a Nijeriya.
A wasu wuraren akan samu litar mai har akan N1,200 wanda har ta kai ga gidajen mai na Kamfanin man fetur na Ƙasa, NNPCL a Kano suka sauya farashinsu zuwa N904 duk lita ɗaya.
Zanga-zangar, wacce aka gudanar a yankin gadar Dangi sakamakon fusata da ƴan adaidatar suka yi, ta haifar da cinkoson ababan hawa wanda har ta kai ga an shafe tsawon sa’o’i a kai.
Hakan ya kuma sanya wasu da dama sun haƙura da zirga-zirgarsu sun shiga sahun masu yi, yayin da wasu kuma suka bi dogayen layuka a gidajen mai.
Sannan, fasinjoji su ma sun koka game da yadda tashin farashin ya shafi adadin da suka saba biya na zirga-zirga a adaidata sahu da sauran nau’ukan ababan hawa.
