Nijeriya ta samu lantarki na megawat 5,313 mafi yawa a shekaru uku

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ministan Wutar Lantarki na Nijeriya, Cif Adebayo Adelabu ya bayyana cewa, Hukumar Samar da Wutar Lantarki ta Nijeriya, ta samar da lantarkin da ya kai megawatts 5,313, mafi yawa a cikin shekaru uku da suka gabata.

Ministan ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi a wani taron da ya gudana a birnin Beijing na ƙasar Chana, a jajibirin buɗe taron ƙolin haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen Afirka da ƙasar Chana a ranar Talata.

Adelabu ya yi kira ga Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki da su yi amfani da damar wajen ɗaukar ƙarin lantarki don hana ɗaukewar lantarki a Nijeriya.

A yayin taron, Gwamnatin Tarayya ta kuma rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna biyu da wani kamfanin ƙasar Chana mai suna Mutual Commitment Company Limited.

Hukumar samar da wutar lantarki ta Karkara (REA), wata hukuma ce ta ma’aikatar wutar lantarki ta tarayya ce ta ɗauki nauyin taron.

Waɗanda suka halarci bikin wajen wakiltar Nijeriya sun haɗa da Ministan Wutar Lantarki, Cif Adebayo Adelabu da Manajan Daraktan REA, Abba Aliyu.

Yayin da ya ke jawabi a wajen bikin da ya gudana a birnin Beijing a jajibirin buɗe taron haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen Afirka da Sin, Adelabu ya ce taron na rattaba hannu kan yarjejeniyar na da matuƙar muhimmanci kuma zai tasya a matsayin ranar da za a riƙa tunawa ga Nijeriya.

Ya ce, rattaɓa hannu kan yarjejeniyar na da muhimmanci ga abubuwa da dama.

By ukarofi