Jonathan ya je ziyarar ta’aziyyar mahaifiyar tsohon shugaban ƙasa Yar’adua

Spread the love

Daga Umar Garba a Katsina

Tsohon shugaban Najeriya, Dakta Goodluck Ebele Jonathan, ya kai ziyarar ta’aziyyar rasuwar Hajiya Dada Musa Yar’adua.

Gwamnan jihar Katsina, Mallam Dikko Umar Raɗɗa ne ya tarbi Jonathan a filin sauka da tashin jiragen sama na Mallam Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina, a ranar Asabar.

Jonathan ya kasance mataimakin marigayi shugaba Yar’adua daga shekarar 2007 zuwa 2010.

Daga bisani ya zama shugaban ƙasa a Najeriya na goma 14, a ranar 5 ga watan Mayu na shekarar 2010 bayan rasuwar Umaru Musa Yar’adua.

By Babaji