Gina famfunan tuƙa-tuƙa a Sakkwato kan Naira biliyan 1.2: Tsakanin sani da rashin sani

Spread the love

Daga ALƘALAMIN MARUBUCIYA – BILKISU YUSUF ALI KANO

A kwanakin baya, gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Dakta Ahmad Aliyu ya yi wata magana kan haƙa rijiyar ‘borehole’ wanda akan adadin kuɗin da ya faɗa, sai aka yi masa ca, aka fara yaɗa farfaganda har abin ya zama abin zolaya ga waɗanda suka jahilci mai gwamna yake nufi da abin da gwamna zai yi.

Faɗin za a yi borehole ya sa masu ƙaramin sani suka ɗauka borehole ce irin wanda aka saba yi a gidana da gidanka. Injiniyoyin kirki da yake sana’arsu ce haƙa borehole, ka ji sun yi magana? To ba su ce komai ba saboda sun san borehole kala-kala ce kuma kuɗi–kuɗi ce, ta danganta da ina za a gina ta da wanda zai gina ta da kuma amfanin da za ta yi. Wato waɗanda za su amfana da ita.

Bari na ba ku misali:

Borehole irin ta gidanka da gidana in za a yi ta ana haƙa ta ne ko dai a cikin gida ko a waje kuma ta ba wa cikin gida ruwa da ƴan fanfuna a ƙofar gida. Wannan ba za ka haɗa kuɗinta da borehole ɗin da za ka yi wanda za ta ba wa unguwa ko gari ruwa ba.

Ana borehole ɗin zamani mai aiki da ‘solar da panel’. Shi kansa panel din ya danganta daga ɗaya har 100. Bayan panel akwai tankuna na ƙarfe da ƙarafunan da ake ɗora tankin waɗanda duka su ma kuɗi ne wanda kai Mista ‘lay man’ ba ya cikin tsarin borehole ɗinka mai ƙaramin ƙarfi.

Daga inda za a yi borehole ɗin zuwa inda za a janyo a kai ruwan, ka san mita nawa ce? ba ka da wannan adadin amma ka ke jayayya akan kuɗin? Ba na mantawa a Kano a shekarun baya, an taɓa irin wannan cecekucen akan za a yi borehole a Audu Baƙo Secretariat akan kuɗi miliyan 27 a ma wancan lokacin kuma ko a lokacin da aka fito da kuɗin dalla-dalla, sai aka ga ma ashe sai an yi ciko, bare a Naira irin ta yau ko Dala irin ta yau.

Hatta ‘pipe’ da za a saka, zurfinsa a borehole da ake yi a gida ba ya fin mita hamsin zuwa sittin kuma a samu ruwa wanda zai isa buƙatun mutanen gidan. Ba za ka haɗa kuɗinsa da irin wannan borehole ɗin da gwamnan Sakkwato ya ke bayani ba wanda za a yi mita ɗari biyu har zuwa ɗari hudu a ƙasa saboda adadin waɗanda za su amfana da ruwan da iya nisan da ake son a kai ruwan da kuma ƙarko ko ‘quality’ na aikin da ake buƙata ruwan ya kai don amfanin al’umma. A dai ɓangaren pipe ɗin, shi ma inci-inci ne don haka irin wannan pipe ɗin ana amfani da inci biyar ne maimakon pipe mai inci ɗaya ko biyu da ake amfani da su a ƙananan borehole. Ka da kuma a manta wurin da za a yi irin wannan borehole ɗin ya na da bambanci daga wuri zuwa wuri. Sokoto kowa ya san ta na kusa da ‘Sahara’ ne don haka inda za a haƙa a samu ruwa, ya na da bambanci da inda za a yi a Kano ko Jigawa ko Bauchi. Hatta motocin da suke haƙa borehole ɗin, sun bambanta da waɗanda ake yi da su a wasu jihohi da garuruwa.

Don haka, don an ce za a yi borehole kan Naira biliyan 1.2 guda 24, bai kamata ya zama abin surutu da ce-ce-ku-ce ba, kamata ya yi a tsaya a ga wane irin borehole za a yi tukunna.

Ya kamata adawar siyasa da ma waɗanda su ba adawar suke ba, fatansu kawai su ga kuskure su yaɗa, to ya kamata su jira. Bahaushe ya na cewa “komai gaggawar Ungozoma, ta jira dai a haihu.”

Don haka, Ahmad Aliyu a dai yanzu yana kan aiki bai yi kuskure ba a faɗin za a yi sababbin borehole ne da kuɗin kuma za a yi masu inganci ne da nisan zango. Hatta pump machine za a yi amfani da ‘grundfos submersible pump series five ne AC DC’. Don haka yana da bambanci da wanda ake amfani da shi yau da gobe a gidaje da unguwanni.

Da kyakkyawan fatan duk inda matsalar ruwa take in dai waɗannan borehole sun tabbata, to za a yi sallama da matsalar da yardar Allah. Allah ya sa mu dace, Amin.

By Babaji