Ƙungiyar MOPPAN ta ƙaddamar da kwamitin zaɓe

Spread the love

Majalisar gudanarwa ta ƙungiyar MOPPAN ta gudanar da wani taro mai muhimmanci wanda shugabanta, Alhaji Habibu Barde ya jagoranta a garin Abuja.

Taron wanda mambobi daga sassa daban daban na ƙasar suka halarta ya tattauna batutuwa masu matukar muhimmanci kamar yadda sanarwar mai ɗauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na ƙungiyar Al-Amin Ciroma ta bayyana.

An ƙaddamar da kwamitin zaɓe na mutum 13 waɗanda za su jagoranci shirin zaɓen ƙungiyar da a ke sa ran a gudanar a watan Janairu 2025.

Majalisar ta amince da Alhaji Bala Mu’azu a mastayin ciyaman na kwamiti tare da Nasiru S. Gwangwazo a matsayin sakatare na kwamitin.

Sauran manbobi sun haɗa da Alhaji Abdul Amart, Mallam Umar Uk, Hajiya Umma Shehu da Hajiya Hadizan ( saima) Mohammed waɗanda za su wakilci masana’antar Kannywood.

Saura sun haɗa da Alhaji Ado Ahmad Gidan Dabino, Alhaji Hamisu Jibrin Goma, Alhaji Umar Rabi da Alhaji Ado Mohammed wanda dukkansu zasu wakilci shiyyar Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da kuma Arewa ta tsakiya.

Taron ya bayyana cewa Alh Habibu Barde wanda shine shugaban ƙungiyar yanzu, Alh Salisu Mu’azu wanda shine matsayin sakatare da Alh Bala Mu’azu Kufaina wanda shine ma’ajin ƙungiyar sun bayyana ba za su tsaya takara ba a zaɓen da zai gudana.

Shugaban ƙungiyar ya umarci dukkanin reshen jihohin da basu gudanar da zaɓukan su ba da su yi haka daga nan zuwa watan Nuwamba domin rashin yin haka ba zai basu damar kawo masu zaɓe ba.

Daga ƙarshe ƙungiyar ta bayyana ranar 24 ga Oktoba domin yin wani taron wanda za a rantsar da ƴan kwamitin domin su cigaba aiki ba ƙaƙƙautawa domin ganin an samu sahihin zaɓe da kowa zai yi aminta da shi.

By ukarofi