
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi game da yiyuwar ɓarkewar cutar kwalara a sansanonin ƴan gudun hijira na wucin-gadi da aka kafa a Maiduguri, babban birnin Borno sakamakon ambaliyar ruwa da ta mamaye jihar.
Rahoton da ofishin kula da ayyukan bada agaji na Majalisar Ɗinkin Duniyar ya fitar, yace abubawan da za’a buƙata cikin gaggawa sun haɗa da abinci da tsaro da wurin kwana da kuma tsaftataccen ruwa, inda ya ƙara da cewar wasu daga cikin hanyoyin samun ruwan sun gurɓace kuma na iya janyo ɓarkewar cututtuka irinsu kwalara.
An ruwaito rahoton na cewa, “buƙatun gaggawa da ake dasu sun haɗa da abinci da matsuguni da tsaftataccen ruwan sha, saboda wasu daga cikin hanyoyin samun ruwan sun gurɓace.
Tsaro na daga cikin muhimman abubuwan damuwa, musamman ga yaran da ba sa tare da kowa ko suka rabu da danginsu da tsofaffi da masu buƙata ta musamman.
Wuraren da ambaliyar ta fi shafa a birnin Maiduguri sun haɗa da Gwange da Hanyar Bama da Gidan Namun Daji da Gidan Waya da Sakatariyar Jihar da Titin Legas da Fadar Shehun Borno da babbar kasuwar Maiduguri da yankunan Custom da Gamboru da Budum da Asibitin Ƙwararru da kuma gaba dayan yankin gidan waya.
Mutane da dama sun rasa matsugunansu, sai dai mahukunta, sun shaida cewa wasu sun soma komawa gidajensu.
