Dada ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Bashir Ibrahim Gyarza shine sabon shugaban ƙungiyar jami’an kiwon lafiya ta ƙasa reshen jihar Katsina
Sai Aminu Musa wambai shine ma’ajin ƙungiyar muƙamin da Bashir Ibrahim Gyaza ke riƙe da shi kafin a zaɓe shi sabon shugaban da Sani Yusuf a matsayin sakatare.
Da yake jawabin ban kwana da ƙungiyar tsohon shugaban ta Mannir Mohammed Suleiman ya faɗi wasu nasarorin da ya samu a lokacin yana jagorantar ƙungiyar.
Wasu daga cikin nasarorin da ya samu kamar yadda ya ce sun haɗa shiga harkokin sufuri na ƙungiyar ta hanyar samar da motocin haya domin samar wa ƙungiyar kuɗaɗen shiga
Ƙungiyar ta gina gidan baƙi da aka sanya wa suna kwamred Hussaini Hamisu Guest House domin sauƙaƙawa ya’yan Ƙungiyar wajan masauki da kuma samun kuɗin shiga
Tsohon shugaban ya ƙara da cewa a lokacinsa sun gina shagon abinci da wurin wankin motoci da duk zai sa a sami kuɗaɗen shiga da ba sai ƙungiyar ta fita bara ba.
Sauran su haɗa da taimakawa ya’yan Ƙungiyar da ke aiki a ƙananan hukumomin da ke fama da rashin tsaro kuɗade da kayan binci a kowane wata da dai wasu nasarorin daban daban na bunƙasa rayuwar ya’yan ƙungiyar.
Kwamred Suleiman ya yabawa gwamna Dikko Raɗɗa akan kulawar da yake ba harkan ilimi a jihar.
Yace ya’yan Ƙungiyar na samun albashin su duk wata akan lokaci,haka ma kuɗin fansho da na sallamar aiki duk gwamnan na biya ba ɓata lokaci.
Gwamnan ya gina ɗakin masu allurar ciwon ƙoda da ɗaukaka wasu ƙananan asibitoci zuwa manya a jihar.
A jawabinsa sabon shugaban ƙungiyar Bashir Ibrahim Gyaza ya yabawa shugaban mai barin gado da ya bayyana shi a matsayin haziƙi mai gaskiya da riƙon amma.
Shugaban ya tabbatar da samun cigaba da ba a ga irin sa ba a lokacin shugabancin kwamred Suleiman.
Ya kuma yi alƙawarin ɗorawa inda tsohon shugaban ya tsaya na inganta rayuwa da aikin ya’yan Ƙungiyar a jihar baki ɗaya .
