Fafaroma ya yi tir da mutuwar ƙananan yara a Gaza

Spread the love

Francis ya ce, harin bama-bamai na IDF ta kai a makarantu a Gaza a ƙarƙashin ‘zaton’ mafakar ‘yan Hamas ne “mummuna ne.”

A ranar Juma’ar da ta gabata ne Fafaroma Francis ya yi tir da mutuwar ƙananan yaran Falasɗinawa a hare-haren da sojojin Isra’ila suka kai a Gaza, yana mai cewa harin bama-bamai a makarantu, kan “zaton” da ake yi na kai wa ‘yan Hamas hari, abu ne mai muni.

A hanyar sa ta komawa Roma daga Singapore, Fafaroma ya nuna shakku kan son kai ƙarshen yaƙin da ƙasashen biyu ke nunawa, inda ya ce, ba ya tsammanin Isra’ila ko Hamas, a yanzu da yaƙin ya kai watanni 11 a tsakaninsu, na ƙoƙarin kawo ƙarshen rikicin.

Fafaroma ya ce “Ina mai bayar da haƙuri akan abinda zan faɗa, amma gaskiya ba na jin suna ɗaukar matakan samar da zaman lafiya.”

Yayin da yake magana a wani taron manema labarai da ya yi bayan wani balaguron kwanaki 12 da ya yi a kudu maso gabashin Asiya da Oceania, Francis ya ce, yana magana ta wayar tarho da membobin Cocin Katolika a Gaza “kowacce rana” kuma “suna gaya mani munanan abubuwa, abubuwa masu tsanani.”

“Idan ka ga gawarwakin yaran da aka kashe, a ƙarƙashin zaton cewa akwai wasu ‘yan daba, an jefa bam a makaranta, wannan abu ne mai muni,” in ji Fafaroma mai shekaru 87.

Isra’ila ta ce, ƙungiyoyin ta’addanci na Gaza a kai a kai suna gudanar da ayyukansu ta hanyar amfani da makarantu da sauran wuraren fararen hula, suna amfani da waɗanda ba su ji ba ba su gani ba a matsayin garkuwa da mutane da manufar ƙara asarar fararen hula a lokacin yaƙin. Ta ce tana ɗaukar matakan tabbatar da cewa hare-haren da take kaiwa a irin waɗannan wuraren na kan mayaƙan ne da kuma taƙaita illa ga fararen hula.

Fafaroma wanda ya goyi bayan kiran tsagaita buɗe wuta a rikicin da kuma sakin Isra’ilawa da Hamas ke garkuwa da su, ya ce: “Wani lokaci ina ganin yaƙi ne da ya yi yawa, ya yi yawa.”

Yaƙin Isra’ila da Hamas dai ya samo asali ne sakamakon harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba, lokacin da ‘yan ƙungiyar Hamas suka kashe mutane 1,200 galibi fararen hula, tare da ɗaukar 251 suka yi garkuwa da su, kamar yadda ita Isra’ila ta faɗa.

Ma’aikatar lafiya ta Gaza a ƙarƙashin Hamas ta ce, sama da mutane 40,000 ne aka kashe a yankin ko kuma ake kyautata zaton sun mutu a faɗan ya zuwa yanzu, ko da yake ba za a iya tantance adadin ba, kuma bai bambanta tsakanin fararen hula da mayaƙa ba. Isra’ila ta ce, ta kashe wasu mayaƙa 17,000 a yaƙin da kuma wasu ‘yan ta’adda 1,000 a cikin Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba.

Majalisar ɗinkin Duniya ta faɗa a jiya Alhamis cewa, yaƙin ya ɓarnata tattalin arzikin Gaza, ya ruguza shi.”

Fafaroma ya yi magana kan wasu batutuwa da dama yayin taron manema labarai na mintuna 40. Ya soki manufofin tsohon shugaban Amurka Donald Trump da mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris, ya kuma ce ‘yan ɗarikar Katolika na Amurka dole ne su “zaɓi mafi ƙarantar mugunta” idan za su kaɗa ƙuri’a a watan Nuwamba, ba tare da yin karin haske ba.

Francis ya kuma ce, yarjejeniyar da ɓatican ta ƙulla da Chana kan naɗin limaman Cocin Katolika a ƙasar na nuna sakamako mai kyau, wanda ke nuni da cewa kusan za a tsawaita lokacin da ake shirin sabunta wannan.

Fafaroma ya ce, sakamakon yarjejeniyar 2018, inda ƙasar Sin ta samu wasu bayanai kan zaɓen limaman Cocin Katolika, “yana da kyau.”

“Na yi farin ciki da tattaunawa da ƙasar Sin,” inji Fafaroma.

‘Yan Katolika masu ra’ayin mazan jiya sun yi kakkausar suka ga yarjejeniyar da cewa ta miƙa wa Chana iko da yawa. Fadar ɓatican ta ce yarjejeniyar ta warware rarrabuwar kawuna da aka shafe shekaru da dama ana yi tsakanin wata majami’ar ƙarƙashin ƙasa da ta yi rantsuwar biyayya ga fadar ɓatican da kuma ƙungiyar kishin ƙasa ta Katolika da ke karkashin kulawar gwamnati.

Ba a tablɓa buga yarjejeniyar ba, amma jami’an diflomasiyya ne kawai suka bayyana hakan. Fadar ɓatican ta ce, Fafaroma na da ikon yanke hukunci na ƙarshe wajen naɗa limaman Cocin Chana.

Fafaroma ya kuma musanta rahoton da kafafen yaɗa labaran Faransa suka bayar na cewa zai je birnin Paris a watan Disamba domin sake buɗe Cocin Notre Dame.

Wata ƙaramar kafar Faransa ta ba da rahoton cewa, Fafaroman zai je bikin buɗe babban Cocin na ranar 8 ga Disamba, shekaru biyar bayan wata mummunar gobara. Fafaroma ya kuma ce hat yanzu bai riga ya gama yanke hukuncin tafiya Argentina ko kuma ƙasarsa ta haihuwa. 

“Ina so in je,A amma har yanzu ba a yanke shawarar ba, akwai wasu abubuwa da za a fara warwarewa,” inji Francis, wanda shi ne Fafaroma na farko daga Amurka, wanda kafin haka, ya yi zama babban limamin Cocin Buenos Aires.

Fafaroman ya ce, idan ya je Argentina, zai so ya tsaya kan hanyar Rome a tsibirin Canary, wani yanki mai cin gashin kansa na Spain da ke gaɓar tekun Arewa Maso Yammacin Afirka. 

Sanannen wuri ga baƙin haure da ke amfani da hanyar wurin tsallaka tekun Atlantika don isa Turai. 

Kula da baƙin haure ya kasance babban jigon sarautar Francis na shekaru 11. Ya kai ziyararsa ta farko a matsayinsa na Fafaroma a tsibirin Lampedusa na Italiya, inda ya fuskanci kwararar baƙin haure.

“Ana cikin wani halin a wurin da baƙin haure, waɗanda ke zuwa ta teku,” inji shi game da Canaries. “Kuma ina so in kasance kusa da gwamnati da jama’a.”

An kuma tambayi Francis game da cin zarafin limaman Cocin Katolika, da kuma batun wani limamin Cocin Faransa, da aka fi sani da Abbe Pierre, wanda aka daɗe ana shagulgulan bikinsa da mutanen da ba su da matsuguni, amma daga baya aka bayyana cewa an zarge shi da yin lalata da aƙalla mata bakwai. Ya rasu a shekara ta 2007.

ƙungiyar da Pierre ya kafa, Emmaus, ta bayyana karin shaidu 17 akan marigayi firist a ranar 6 ga Satumba.

Fafaroman ya ce, bai san lokacin da fadar ɓatican ta fara sanin wannan zargi ba. “Tabbas, bayan mutuwarsa, amma a da, ban sani ba,” inji Francis.

By ukarofi