Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Jihar Jigawa ta ce ta shirya tsaf domin tinkarar zaɓen ƙananan hukumomi da za a gudanar a ranar 5 ga Oktoba 2024.
Shugaban hukumar zaɓen mai zaman kanta Malam Auwalu Harbo ya sanar da haka a wani taron manema labarai da hukumar ta shirya a ofishin ta.
Ya ce zuwa lokacin da yake zantawa da manema labaran sun sami adadin jam’iyyu 11 da aka tantance za su shiga zaɓen da za a gudanar a cikin makon gobe.
Ya cigaba da cewar nan bada jimawa ba zasu kafe sunayan dukkan yan takara da hukumar zaɓen ta riga ya ta tantancesu a dukkan jam’iyyun.
Ya kara da cewar yanzu Kashi saba’in cikin ɗari na kayan zaɓe da hukumar ta ke buƙata domin aikin zaɓen yana hannun ta.
Kuma za su dauki turawan zaɓe a ɗaukacin ƙananan hukumomin jihar 27 inda za a ɗauki mutum uku a kowacce ƙaramar hukumar, Kuma za a ɗauki ma’aikata 4,542 a ɗaukacin akwatinan zaɓen jihar.
Harbo ya ƙara da cewar adadin ma’aikatan zaɓen da hukumar zaɓen za ta ɗauka har da masu aikin amsar sakamakon zaɓe da yawan su ya kai mutane 14,794.
Yaci gaba da cewar tuni sun ɗauki matakin da za su gudanar da zaɓen cikin lumana da kwanciyar hankali kuma hukumar ta shirya tsaf domin ganin ta yi aiki da jami’an tsaro domin ganin anyi zaɓen cikin kwanciyar hankali.
Ya ƙara da cewar a cikin jerin jam’iyyun da suka shiga zaɓen har da PDP mai ƴan takarar ciyamomi mutum biyu a Kafin Hausa da Gwaram sai Kuma jam’iyyar NNPP da ta tsayar da na ta a Ringim da Malam Madori.
Yayin da sauran jam’iyun suka tsayar da kansiloli a wasu mazaɓu da ke faɗin jihar, ita jam’iyyar APC mai mulki babu ƙaramar hukumar da ba ta da ‘yan takarar a dukkan mazaɓun jihar.
Da ya juya batun ƙarar da ADP ta shigar a kotu yace kotu ta yi masu adalci akan waccan Sharia da suka shigar suna ƙalubalantar zaɓen.
