Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina za ta gudanar da jarrabawa ga shugabanni da mataimakan su na makarantun gaba da firamare a faɗin jihar.
Wannan mataki da gwamnati ta ɗauka ya biyo bayan rashin kataɓus da ɗaliban jihar suka yi a jarabawar NECO na wannan shekara.
Kwamishinan ilimi a matakin farko Hajiya Zainab Musawa ta sanar da haka a hira da manema labarai a ofishin ta.
Ta ce jarrabawar shi zai taimakawa gwamnati wajen sake naɗa shugabannin makarantun bisa cancanta.
Haka kuma kwamishinan ilimin ta sanar da cewa ma’aikatar ta za ta dawo da karatun dare ga duk ɗaliban da ke shekaran karshe na kammala karatun su.
Ta ce wannan karatun dare da ma’aikatar za ta sake dawo da shi zai mai da hankali ne wajan horas da ɗaliban koyon turanci da lissafi.
Kwamishinan ta yaba da ɗaliban jihar da suka zauna jarabawar shekarar ƙarshe na NECO da jihar ta zo na 6 wajan samun sakamakon credit biyar.
Hajiya zainab sai ta faɗi wasu nasarorin da gwamnatin Dikko Raɗɗa ta samu wajan harkar ilimi a jihar,sun kuwa haɗa da samar da kayayyakin karatu a makarantu a faɗin jihar, kwamishinan ta ce.
Ta ƙara da cewa gwamnatin Dikko Raɗɗa ta kuma ɗauki malaman makarantu na firamare da na gaba da firamare guda 7000 da ƙarin wasu malaman da ta ɗauka daga baya .
