Gwamnatin tarayya ta amince da ƙarin alawus alawus na masu hidimar ƙasa zuwa N77,000 duk wata daga Yuli 2024.
A cewar wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun muƙaddashin daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na NYSC, Caroline Embu, a ranar Laraba 25 ga watan Satumba, 2024, amincewar na ƙunshe ne a cikin wata wasiƙa daga hukumar albashi da kuɗaɗen shiga ta ƙasa, mai kwanan wata 25 ga Satumba 2024 tare da sanya hannu. da shugaban hukumar Mista Ekpo Nta ya yi.
Kafin ƙarin kuɗin, an riƙa biyan masu hidimar ƙasan alawus-alawus na N33,000 duk wata biyo bayan sake duba mafi ƙarancin albashi zuwa N30,000 a shekarar 2019.
Ku tuna cewa Shugaba Bola Tinubu ya rattaɓa hannu kan sabuwar dokar mafi ƙarancin albashi a ranar 29 ga Yuli, 2024.
Dokar ta tanadi Naira 70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.
