Ba za mu bari Isra’ila ta kori Falasɗinawa ba – Sarkin Jordan 

Spread the love

Sarkin Jordan Abdullah na biyu ya ce akwai yiwuwar ƙasarsa ta zama tudun-mun-tsira ga Falasɗinawa, yana mai gargaɗin cewa, raba su da muhallansu da Isra’ila ke yi ka iya zama laifukan yaƙi.

Shi ma Sarki Abdullah na magana ne a gaban shugabannin ƙasashen duniya a zauren Majalisar ɗinkin Duniya, yayin da ya jaddada cewa, ba za su taɓa bari a sauya wa Falasɗinawa matsugununsu ba zuwa Jordan kamar yadda wasu masu tsattsauran ra’ayi ke buƙata.

Sarkin ya ce, Jordan ba za ta amince a raba Falasɗinawa da muhallansu ba saboda haka tamkar aikata laifukan yaƙi ne a cewarsa.

Jordan dai ta haɗa iyaka da Yamma da Kogin Jordan da Isra’ila, sannan tana da ɗimbin Falasɗinawa da ke zaune a cikinta.

Sarkin ya kuma roƙi shugabannin ƙasashen duniya da su agaza wa mutanen Falasɗinu da ke cikin matsananciyar buƙatar abinci da ruwan sha da magunguna da sauran kayayyakin buƙatar ɗan adam.

“Duniyarmu ta gaza ta fannin siyasa, amma bai kamata tausayinmu ya gaza isa ga mutanen Gaza ba,” Inji Sarki Abdullah.

By ukarofi