Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya caccaki Majalisar ɗinkin Duniya saboda rashin ɗaukar mataki kan yaƙin Gaza, yana mai zargin Isra’ila da mayar da yankin Falasɗinu a matsayin maƙabartar binne mata da ƙananan yara.
Kazalika shugaba Erdogan da ke magana a zauren taron Majalisar ɗinkin Duniya a birnin New York na Amurka, ya nuna goyon bayansa ga Lebanon wadda Isra’ila ke ci gaba da yi mata luguden wuta da nufin kakkaɓe mayaƙan Hezbollah, inda kuma ya soki gwamnatin Benjamin Netanyahu da ƙoƙarin jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin yaƙi.
Ba ƙananan yara kaɗai ke mutuwa ba a Gaza, hatta tsarin Majalisar ɗinkin Duniya shi ma yana mutuwa a yankin. Inji Erdogan
Erdogan ya kuma ɗiga ayar tambaya kan sahihancin ayyukan ƙungiyoyin ƙare hakkin bil’adama na duniya, yana mai cewa, shin ba mutane ba ne ke rayuwa a Gaza da kuma Gabar Yamma da Kogin Jordan?
Har ila yau, shugaban na Turkiyya ya caccaki Kwamitin Sulhu na Majalisar ɗinkin Duniya kan gazawarsa wajen bayar da umarnin dakatar da yaƙin Gaza, inda ya ce mambobin kwamitin sun zura ido suna kallon yadda ake aiwatar da kisan kiyashi a yankin.
Erdogan ya kuma kwatanta Netanyahu da jagoran sojojin Nazi, Adolf Hitler, inda ya buƙaci ƙasashen duniya da su yi duk mai yiwuwa domin dakatar da shi daga kashe-kashen da yake yi a cewarsa.
Hukumomin Gaza sun ce, aƙalla mutane 41,467 ne Isra’ila ta kashe a jerin hare-haren da take ƙaddamarwa a yankin tun bayan da Hamas ta kai wani hari a ranar 7 ga watan Oktoban bara cikin Isra’ila wanda ya halaka mutane 1,215. RFI
