Daga DAUDA USMAN a Legas
Sarkin Hausawan Kuje ta ƙaramar hukumar Amuwo Odọfin dake cikin birnin Ikko, Dakta Alhaji Suleiman Rabiu kuma kakakin majalisar sarakunan Hausawa mazauna jihohin Kudu da yammacin Nijeriya, ya shawarci Gwamnatin Tarayya da sauran gwamnatocin jihohin ƙasar nan da su tausaya su duba mutanen da iftila’in ambaliyar ruwa ta shafa a garin Maiduguri ta jihar Borno.
Sarkin al’ummar Hausawan na Kuje Dakta Alhaji Suleman Rabiu ya bada wannan shawara ce a Legas a lokacin da yake zantawa da Jaridar Bueprint Manhaja dangane da wannan al’amari, inda Sarkin ya cigaba da cewa dangane da tsadar rayuwar da al’umma suke ciki ya kamata Gwamnatin Tarayya da sauran gwamnatocin jihohin ƙasar da su tausayawa su kawo wa waɗan nan mutane ɗauki da abubuwan da za su cigaba da inganta harkokin rayuwarsu ta yau da kullum.
Ya ƙara da cewa bai kamata ba irin wannan al’amari ya faru na ɓacin rai wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan ɗumbin al’umma da dukiyoyinsu gwamnati ta ce ba za ta taka rawar gani ba. Ya ce kuma yana mai gabatar jajensa ga mai Martaba Sarkin Borno Alhaji Garbai Shehu da Gwamnan jihar Farfesa Baba Umara Zulum da sauran al’ummar da suka rasa rayukan ‘yan uwa da dukiyoyinsu, da fatan Allah Ubangiji ya jiƙan waɗanda suka rasa rayukansu ya sanya Aljanna ce makomar su bakiɗaya.
Ya ce su kuma waɗanda suka tafka asarar gidaje da dukiyoyinsu yana mai fatan Allah Ubangiji ya mayar masu da alheri game da dukiyoyin da suka rasa.
Sannan kuma kakakin majalisar sarakunan Hausawan mazauna jihohin Kudu da Yammacin Nijeriya ya cigaba da jawo hankulan sarakunan al’ummar Hausawa mazauna jihohin Kudu da yammacin Nijeriya da su cigaba da ɗora mabiyansu bisa kan turbar zaman lafiya domin ciyar da ƙasar nan gaba.
Haka zalika ya cigaba da yin kira ga ‘yan kasuwa masu sayar da kayan a binci da su sani cewa tsadar rayuwa ta zama ruwan dare mai gama duniya, amma a cewarsa wani abin ‘yan kasuwa suke ƙara wa miya gishiri, ya ce akan haka yake ganin ya kamata su ma ‘yan kasuwa masu kasuwancin kayan abinci a Nijeriya suma suna da muhimmiyar rawar da za su taka a wajen kawo wa ‘yan Nijeriya sauƙi ta fuskar samun rangwamen farashi wajen sayan kayan abinci.
ƙarshe ya isar da saƙon ta’,aziyarsa ga hukumar gidan rediyon Nijeriya ɓON FM Legas dangane da rasuwar Ahmed Isah Koko shahararren ɗan jaridan nan kuma fitaccen mai karanta littattafan Hausa a waɗansu kafofin yaɗa labarai na ƙasar, fatan Allah Ubangiji ya jiƙansa ya gafarta masa amin.
