Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Majalisar Dokokin Jihar Kogi ta nemi Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya gaggauta tsige Shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukoyede, wanda ta zarga da kawo ruɗani a batun binciken tsohon gwamnan jihar, Yahaya Bello.
Sun yi tir da abin da shisshigin kutsawa Gidan Gwamnatin Kogi da ke Abuja, wanda EFCC suka yi har suka yi harbi a cikin gidan.
EFCC ta afka cikin Gidan Saukar Baƙi na Gwamnatin Kogi a Abuja cikin makon jiya, domin kamo Yahaya Bello, wanda ke cikin gidan.
To sai da ‘yan majalisar sun ce EFCC ta keta doka da ta yi harbi a cikin gidan, domin hakan da suka yi, yunƙuri ne na kashe Gwamnan Kogi da ke kan mulki a yanzu Ahmed Ododo.
Kakakin Majalisar Kogi, Aliyu Yusuf, ya ce “abin da EFCC ta yi ya nuna irin yadda hukumar ba ta girmama tafarkin dokokin ƙasa, ta saka siyasa a batun yaƙi da cin hanci da rashawa.
A zaman ta ranar Litinin, majalisar ta yi kira ga Shugaba Tinubu ya gaggauta tsige Shugaban Hukumar EFCC, Olukoyede, “saboda bai ƙware wajen yaƙi da cin hanci da rashawa ba, ya saka siyasa a cikin aikin.”
Majalisar ta ce abin da EFCC ta yi a Gidan Gwamnatin Jihar Kogi a Abuja, zai iya lahanta Gwamna Ododo da tsohon gwamnan jihar, Yahaya Bello.
‘Yan Majalisa irin su Akus Lawal, Jacob Olawunmi da kuma Abu Jibril mai wakiltar ƙaramar hukumar Ajaokuta, duk sun ma nemi a gaggauta gurfanar da Shugaban EFCC a hukunta shi.
Jibril ya ce Shugaban EFCC da kan sa ya umarci jami’an sa su yi harbi a cikin Gidan Gwamnatin Jihar Kogi a Abuja, inda tsohon gwamnan ya nemi mafaka.
