Lokacin soke tallafin mai a Nijeriya ya yi — Ɗangote

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Attajirin Afirka, Alhaji Aliko Ɗangote, ya ce lokaci ya yi da gwamnatin Nijeriya za ta soke tsarin biyan tallafin man fetur.

A wata hira da ya yi da kafar Bloomberg a ranar Litinin, ɗangote wanda shi ne mamallakin matatar mai na ɗangote, ya ce tallafin man fetur zai sa gwamnati ta “biyan kuɗaɗen da bai kamata ta biya ba,” don haka akwai buƙatar a soke shi.

Ya nace cewa gwamnatin Bola Tinubu ba za ta iya ci gaba da biyan tallafin man fetur ba.

A yayin jawabinsa na karɓar aiki a a ranar 29 ga Mayu, 2023, Shugaba Tinubu ya ayyana kawo ƙarshen tallafin man fetur.

Amma cikin gaggawa ya maido da shi bayan da hauhawar farashin kayayyaki ya ƙaru.

An ɗauki wani mataki na kawo ƙarshensa a farkon watan Satumba lokacin da aka sassauta farashin man fetur, amma kuma sai ya kansace farashin ya gaza matakin kasuwa.

Amma ɗangote ya ce: “Ina ganin lokaci ya yi da ya kamata a cire tallafin domin duk ƙasashe da ku kusa da mu sun soke shi.

“Farashin man fetur ɗinmu ya kai kusan kashi 60 na farashin ƙasashen da ke makwabtaka da mu kuma muna da iyaka da su, don haka ba ya ɗorewa.

“Gwamnati ba za ta iya biyan tallafin ba.”

Shawarar ɗangote ta biyo bayan fara aikin dakon man fetur daga matatarsa a baya-bayan nan, da kuma ƙarin farashin litar man zuwa N950 a jihar Legas, da kuma sama da N1000 a yankin Arewa.

A cewarsa, samar da man fetur daga matatarsa ​​zai taimaka wajen rage matsin lamba a kan Naira, sannan kuma ya tabbatar da mallakar rijiyoyin mai guda biyu da ake sa ran za a samu a watan gobe.

Ya ce: “Tallafi lamari ne mai matukar muhimmanci. Da zarar ka ba da tallafin wani abu to mutane za su tsuga farashi sannan gwamnati za ta biya abin da bai kamata ta biya ba. Lokaci ya yi da za a kawar da tallafin.”

By ukarofi