‘Yan sanda a Imo sun kama mutanen da ake zargi da sayar da ƙananan yara 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar ‘yan sanda a jihar Imo ta kama wasu mutane huɗu da ake zargi da safarar ƙananan yara, inda ake zarginsu da sayar da yara kan Naira Miliyan 1.

Manhaja ta rawaito cewa mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda a jihar, Henry Okoye, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.

Mista Okoye, ya ce mutanen waɗanda suka haɗa da maza 2 mata 2 suna sace yara daga wurin iyayensu.

Mai magana da yawun ‘yan sandan ya ce an kama mutanen ne bayan bibiyarsu a maɓoyarsu a jihar.

Sai dai bai bayyana lokacin da aka kama su ba da wurin da suke ɓuyan.

Waɗanda ake zargin sun haɗa da Ifeoma Anyunwu mai shekaru 41 da Chilbuzor Lucky mai shekaru 42 sai Charity Kalu wacce ke da shekaru 24 waɗanda dukkan sh ‘yan asalin jihar Abia ne wacce ke maƙotaka da Imo.

Na cikon hudun shi ne Isidore Ozioma wacce take a garin Umuhu a jihar ta Imo.

“Bincike ya nuna cewa waɗanda ake zargin sun yaudari yaran zuwa babur ɗin su a yayin da suke wasa a waje, inda daga nan suka kai su wani ɓoyayyen wuri a garin Aba inda suka sayar da su kan Naira Miliyan ɗaya,” inji mai magana da yawun ‘yan sandan.

An miƙa yaran da aka ceto zuwa ga iyalansu.

‘Yan sandan sun kuma ja hankalin iyaye da su dinga kula da ‘ya’yansu.

By ukarofi