Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kauyen Tokulo da ke ƙaramar Hukumar Bwari a babban birnin tarayya Abuja sun shiga ruɗu sakamakon tsintar gawarwaki guda 12 da aka yi a garin da ake tunanin ‘yan bindiga ne.
Kansilan mazaɓar Igu a yankin, Jerry Alkali ya shaida wa Daily Trust cewa mutane ne suka kira shi da misalin ƙarfe 2 zuwa 3 na daren Litinin, cewa suna ta jin harbe-harbe.
Ya ce, “ranar babu wanda ya iya barci. Da safiya da mutane suka fara zuwa tafiya zuwa gona suka fara ganin gawarwaki a wata hanyar tafiya ƙaramar hukumar Kagarko da ke jihar Kaduna,” in ji shi.
Jaridar mai zaman kanta ta ruwaito cewa mutanen garin sun ce a cikin gawarwakin babu ɗan garin, wanda a cewarsu ke nufin ko dai an kashe a musayar wuta, ko kuma an kashe ne a wani wurin daban, aka kwaso gawarwakin aka kawo ƙauyensu.
Har zuwa lokacin haɗa labarin a a samu kakakin rundunar ‘yansanda Abuja Josephine Adeh a waya ba.
