Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar NDLEA reshen jihar Ebonyi ta bayyana cewa ta kama haramtattun ƙwayoyi masu nauyin kilogiram 115.226 sannan ta kuma kama mutum 149 da suke da alaƙa da safarar muggan ƙwayoyi a cikin watanni uku a jihar.
Shugaban hukumar Peter Ogar ya sanar da haka yayin hira da Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya NAN ranar Laraba a garin Abakaliki.
Ogar ya ce Jami’an hukumar sun yi wannan kamen daga watan Yuli zuwa Satumba a 2024.
Ya ce a tsakanin wannan lokacin hukumar ta kama mutum 82 inda a ciki akwai maza 64 da mata 18 da ake zargin suna safarar muggan ƙwayoyi.
Ogar ya ce ma’aikatan hukumar sun kama masu safarar muggan ƙwayoyi mutum 149 inda a ciki akwai maza 112, mata 37 masu shekaru 26 zuwa 72.
“Daga cikin mutum 149 ɗin da aka kama akwai masu safarar muggan ƙwayoyi da masu ta’ammali da muggan kwayoyi.
Hodar ibilis, ganyen wiwi, codeine, tramadol, Diazepam, methamphetamine, bromazepam, lorazepam, monkey tail, raphynol da dai sauran su na daga cikin kwayoyin da aka kama.
Ogar ya ce kotu ta yanke wa mutum daya hukunci sannan rundunar ta gudanar da taro domin wayar da kan mutane a ƙauyuka da makarantun firamare da sakandare.
Ya ce hukumar za ta ci gaba da zage damtse wajen yaki da sha da safarar muggan kwayoyi a jihar da ƙasa baki ɗaya.
