

Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Talata ne tsohon ɗan Majalisar Wakilan Nijeriya daga Jihar Kano mai suna Farouk Lawan, ya fito daga gidan yari wanda aka garƙame shi na tsawon shekaru biyar sakamakon nema da kuma karɓar Dala 500,000 a matsayin cin hanci.
An kama shi ne da laifin neman cin hancin Dala miliyan 3 daga Attajirin ɗan kasuwan nan mai suna Femi Otedola a lokacin da ya ke shugaban kwamitin majalisa kan binciken badaƙalar tallafin man fetur a shekarar 2012.
Ɗan majalisar ya yi godiya ga Allah (SWT) da kuma ƴanuwa da abokan arziƙi kan gudunmawar da suka bayar har zuwa wannan lokaci da ya shaƙi iskar ƴanci, kamar yadda ya bayyana cikin wata takarda da ke ɗauke da sanya hannunsa.
