
Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Talata ne Kotun Ƙoli ta dakatar da hukuncin ƙarar da wasu jihohi 19 a Nijeriya suka shigar wadda ke ƙalubalantar dokokin da suka bada damar kafa hukumar hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati (EFCC) da wasu guda biyu.
Cikin ƙarar, an samu batun da ke cewa dokar da ta bada damar kafa EFCC da aka yi a 2004 ya samo asali ne daga zaman Majalisar Ɗinkin Duniya inda suka ce ba a bi tsarin da kundin mulkin ƙasa na 1999 ya samar ba.
Sun bayyana cewa, sai samu mafi yawancin mambobin Majalisar Ƙasa sun amince da ƙudirin buƙatar ƙafa hukumar da wasu, kafin a yi hakan, wanda ba a yi ba.
Yayin da ake cigaba da sauraron ƙarar a ranar Talata, jihohin Imo, Bauchi da Osun sun shiga sahun masu shigar da ƙarar yayin da Anambara, Ebonyi da Adamawa suka sanar da janyewa daga ciki.
Mai Shari’a, Uwani Abba-Aji wadda ta gabatar da hukuncin, ta yi watsi da wasu daga cikin batutuwan da ke cikin takardar ƙarar kasancewar sun sha bamban da waɗanda aka gabatar a karo na biyu inda ta dakatar da sauraron ƙarar zuwa wani lokaci.
Jihohin da suka shigar da ƙarar sun haɗa da; Kogi, Kebbi, Katsina, Sokoto, Jigawa, Enugu, Oyo, Benue, Plateau, Cross River, Ondo, Niger, Edo, Bauchi, Imo, Osun, Nasarawa, Ogun da kuma Taraba.
