
Daga BELLO A. BABAJI
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta tsige Farfesa Sani Malumfashi daga muƙaminsa na shugaban hukumar zaɓe ta jihar, KANSIEC sakamakon alaƙarsa da wata jami’yya.
Mai Shari’a Simon Amobeda ya gabatar da hukuncin a ranar Talata bayan da Aminu Aliyu Tiga da jami’yyar APC reshen jihar suka shigar da ƙara akan sa.
Da farko dai, APC ta ƙalubalanci hukuncin da hukumar zaɓen ta yi na sanya Naira miliyan 10 a matsayin kuɗin shiga takarar shugaban ƙaramar hukuma da Naira miliyan 5 ga kujerar kansila a zaɓen ƙananan hukumomin jihar da ke tafe.
