Ƙarya ku ke, babu mai suna Ibrahim da Yahaya a masu taimaka min – Sanata Ashiru ga NDLEA

Spread the love

Sanata Oyelola Ashiru ya musanta zargin da hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) ta yi masa, tana cewa an kama shi da kwayoyi masu haɗari.

NDLEA ta bayyana cewa an kai samame gidan Sanata Ashiru dake Ilorin, Jihar Kwara, kuma an samu miyagun ƙwayoyi a gidan.

Wannan zargi ya biyo bayan bayanin da Sanata Ashiru ya yi a zauren majalisa na cewa hukumar NDLEA tana amsar cin hanci.

Sai dai wata sanarwa da mai taimaka masa na harkokin majalisa, Olaitan Adeyanju, ya fitar ya ce zargin ƙarya ne.

“Abin kamar shirme, domin hukumar NDLEA sai bayan Sanata Ashiru ya yi bayanin a zauren majalisa sannan suka fito da wannan zargi mara tushe.

“A gaskiya, Sanata Ashiru bai taba ɗaukar Ibrahim Mohammed ko Mohammed Yahaya aiki ba kamar yadda NDLEA ta ambata.

“Sanarwar ta ce an kai samame gidan Sanatan dake Ilorin, kuma ba a sami komai da ya saɓa doka ba. Duk gidan an bincika, ba a sami komai da ya saɓawa doka ba. Idan har an samu wasu ƙwayoyi a wurin mutanen da hukumar NDLEA ta ambata, ya dace a tambayi a wace kotu aka gurfanar da su?

“Hakanan, ya zama dole a fayyace cewa Sanata Ashiru bai taɓa aika wani mai taimaka masa ga NDLEA ba domin neman a wanke wani mai suna Tosin Odepidian daga zargin ƙwayoyi. Duk sunayen da hukumar ta ambata, ba wanda yake aiki kai tsaye ko a kaikaice da Sanata Ashiru.

“NDLEA tana da haƙƙin kai duk wanda take zargi da fataucin miyagun ƙwayoyi gaban kotu, maimakon kiran suna da kuma ƙoƙarin yanke hukunci ta kafafen watsa labarai.

“Wannan sanarwa tana da niyyar fayyace gaskiya da kuma gyara duk wata fahimta da ta biyo bayan bayanin da hukumar NDLEA ta fitar.

“Sanata Ashiru yana nan daram wurin hidimtawa mutanen Kwara ta Kudu tare da tsayawa tsayin daka kan gaskiya a ko yaushe wajen neman ingantaccen aiki daga hukumomin tsaro na ƙasarmu.”

By ukarofi