Shugaban ƙasar Kamaru ya bayyana bayan raɗe-raɗin mutuwa

Spread the love

Shugaban ƙasar Kamaru mai shekaru 91, Paul Biya, an gan shi a bainar jama’a a karon farko bayan makonni shida da ake raɗe-raɗin mutuwarsa.

Ɓatan sa daga idon jama’a ya haifar da jita-jitar rashin lafiyarsa, har ma wasu suka yi tunanin ya rasu.

Amma a ranar Litinin da rana, gidan talabijin na gwamnatin ƙasar ya nuna faifan bidiyon isowar shugaban a filin jirgin saman birnin Yaoundé daga wani jirgi da ya taso daga Switzerland.

Gwamnatin ta haramta wa kafafen yaɗa labarai tattauna lafiyar Biya — wanda ya yi mulki tun daga shekarar 1982, ta na mai bayyana hakan a matsayin al’amari mai alaƙa da tsaron ƙasa.

Jita-jitar mutuwarsa ta daɗe tana yawo a wasu lokuta tun sama da shekaru ashirin da suka gabata.

Bidiyon da aka watsa a ranar Litinin ya nuna shugaban cikin kayan sa na yau da kullum, sutura mai tsabta da kuma kalar dattako, yana nuna ƙarfi a jikinsa.

A karon ƙarshe da aka ga Biya shine a ranar 8 ga Satumba, a taron ƙolin ƙasashen Chana da Afrika da aka gudanar a Beijing.

Tun daga wannan lokacin, gwamnati ta fuskanci matsin lamba don ta tabbatar da cewa shugaban yana raye.

Jami’an gwamnati daga bisani sun musanta ikirarin cewa ya mutu, suna mai cewa Biya yana cikin ƙoshin lafiya kuma yana kan ziyarar sirri a Geneva. An san shi da yawan ziyarar birnin na Switzerland.

Bayan isarsa, an tarbe shi da jami’an gwamnati da mambobin jam’iyyar da ke mulki.

Taron mutanen da aka shirya a wasu titunan babban birnin yana nuna cewa gwamnati tana da nufin kawo ƙarshen jita-jitar rashin lafiyarsa.

Bayyanarsa a karo na farko tun bayan jita-jitar mutuwarsa na iya haifar da kira daga cikin jam’iyyarsa ta CPDM domin ya nemi tazarce a wa’adin shekaru bakwai a zaɓen shekara mai zuwa.

By ukarofi