Daga ABUBAKAR M TAHEER
Gwamnatin Jihar Jigawa za ta fara gudanar da shirin Citizen Leads Initiative nan ba da jimawa ba domin bunƙasa harkokin ilimi da koyarwa a jihar. Hakan na ƙunshe ne cikin wata zantawa da ƙwararriyar mai bawa gwamna shawara kan harkokin ilimi Dakta Hauwa Mustapha Ɓaɓura ta Jihar Jigawa kan halin da jihar take ciki na taɓarbarewar harkokin ilimi. Gwamnatin jihar za ta gayyaci sarakuna,yan kasuwa,malamai da masu riƙe da madafun iko domin ciyar da fannin ilimi a jihar.
Shirin Citizen Lead initiative zai kasance wata hanya ta musamman da dukkan ɓangarorin al’ummar daga ciki da wajen jihar za su haɗu domin saka ido, gudanar da bita ga malaman makaratu, ɗalibai, da ma tarukan wayar da kai ga al’ummar dake faɗin jihar ta Jigawa.
Dr. Ɓaɓura ta ƙara da cewa ya zama haƙƙi da Allah ya ɗora mana gaba ɗayanmu yan jihar Jigawa da mu sauke nauyin ilimantar da yayanmu, jikokinmu da yan uwanmu.
Ba dole sai gwamnati ce kaɗai ke da wannan nauyi a kanta ba.
Akwai abun takaici al’umma suna gani wasu ɓatagari su rinƙa ɓarnata kadarorin makarantunmu suna sacewa mu kuma zuba musu ido, wannan babbar illa zai mana ga goben yaranmu.
Dole Sauran al’umma su kula da makarantu, kula da inganci ilimin, saka ido wajen zuwan malamai makarantu domin ta haka ne zamu taro sauran jihohi da ake alfahari dasu wajen cigaban ilimi a ƙasarnan.
A ƙarshe Dakta Hauwa ta ƙara da cewa gwamnatin jihar a Shirye take wajen karɓar shawara daga masana, ƙungiyoyi wajen gudanar da bita ga Malamai, ɗalibai da ma dukkan sauran al’ummar jihar ta Jigawa.
A cikin satin da ya gabata gwamnan Jihar Jigawa Malam Umar Namadi ya ware kuɗi Naira Miliyan 740 domin gina azuzuwa,ɗakunan gwaja-gwaje, banɗaki a wasu makarantun jihar tare da ɗaukan matakin maida yaran dake gararan ba a titina makaranta.
Alƙaluma daga hukumar ilimin bai ɗaya ta jihar Jigawa (UBEC) sun nuna cewa kusan yara dubu 400,000 ne basa zuwa makaranta a faɗin jihar. Wanda hakan yasa take cikin na gaba-gaba a faɗin ƙasar nan.
Ko a shekarar 2022 hukumar kula da asusun kula da ilimin yara na Majalissar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa yara dubu 700,000 ne a jihar ta Jigawa basa zuwa makaranta.
