Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Malaman makarantun firamare 17000 su ka samu horo daban daban akan sanin makaman aiki da yadda zasu inganta koyarwa a jihar.
Shugaban hukumar ilimin firamare na bai ɗaya (SUBEB) Dakta Kabir Magaji ya bayyana haka a taro da yayi da sakatarorin ilimi na ƙananan hukumomi 34 da ke Jihar Katsina.
Ya ce hukumar ta na bada horaswar ne ga malamai domin su san sabbin dabaru na koyarwa ta yadda su ma za su tafi da zamani.
Dakta Magaji ya tabbatar da cewa su ma sauran malaman da ba su sami halartar horon da su shirya nan ba da jimawa ba za su halarta.
Sai ya yi kira ga sakatarorin ilimin da su tantance waɗanda ba su sami zuwa horon ba domin suma su halarta.
Shugaban hukumar ya ja hankalin sakatarorin ilimin da su tabbatar suna sa ido akan malaman firamare na yankin su domin gano waɗanda ba sa zuwa da masu zuwa a makare.
Ya gargaɗi malaman firamare a jihar cewa duk wanda aka samu da baya zuwa aiki ko kuma yana makara da ya kuka da kansa.
Haka kuma Dakta Kabir Magaji yayi kira ga su sakatarorin ilimin da su sa ido ga aikin gine ginan da ake gudanarwa a makarantun jihar da su tabbatar anyi aiki kaman yadda aka tsara.
Yayi gargaɗin cewa hukumar ba zata yadda ace bayan shekara biyu da gina makaranta a dawo ace za ayi wasu gyara gyare
Yawan malaman firamare a jihar ya zuwa yanzu ya kai 30,000.
