Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse
Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa da ke Arewacin Nijeriya ya ƙaddamar da kwamitin da zai binciki musabbabin aukuwar gobarar da ta yi sanadin rasa rayukan al,umma a ƙauyen Majiya da ke ƙaramar hukumar Taura.
Kuma kwamitin shine zai Kula da rabawa al,ummar ƙauyen na Majiya tallafin da jama,a da gwamnatin Jigawa ta kafa sakamakon haɗarin motar mai da ya haifar da mutuwar mutane kimanin 180 a ƙauyen na Majiya da ke ƙaramar hukumar Taura.
Gwamna Namadi ya rantsar da kwamitin mai mutane 25 yau a fadar gwamnatin jihar da ke Dutse a ƙarƙashin jagoranchin DIG Mai Ritaya Hafizu Muhd Inuwa Ringim domin ganin an yiwa kowa adalci .
Gwamna Namadi ya kafa kwamitin domin ya aiwatar da bincike kuma ya sanya ido wajen yadda za a raba wa waɗanda abin ya shafa tallafin
Da yake ƙaddamar da kwamitin Gwamna Namadi yace ya zabo ‘yan kwamitin ne saboda ƙwazon su da cancantar su shi yasa aka naɗa su mambobi a kwamitin.
Saboda haka ya shawarcesu da su yi iyakacin ƙoƙarin su wajen sauke nauyin da aka ɗora musu. Ya kuma hore su da gudanar da aiki bi sa sharuɗan da aka ɗora su a kai .
A nasa jawabin shugaban kwamatin DIG Mai Ritaya Hafizu Muhd Inuwa ya yabawa Gwamna Umar Namadi da ya zakulo su ya naɗa su a cikin mutane mafiya daraja domin su bada tasu gudunmawar wajen bada tallafin.
Yayi alƙawarin cewa kwamitin zai yi aikin shi tsakani da Allah wajen ganin sun sauke nauyin da aka ɗora masu tare da taimakon ‘yan kwamitin sa da za su yi aiki tare.
