
Daga BELLO A. BABAJI
Hukumar Kula da Babbar Birnin Tarayya, Abuja, ta aika da saƙon gargaɗi ga mabaratan da ke gararamba a titina da su guje wa cigaba da yin hakan don kar jami’an tsaro su kama su.
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayyana hakan a Katampe a lokacin da ya ke ƙaddamar da aikin titin da zai kai ‘Judges’ Quarters’.
Ya ce, adadin waɗanda ke zama gefen hanya da sunan bara ya fara yawa wanda kuma hakan barazana ce ga tsaro a birnin.
Daga nan ne sai ya bada wa’adin ranar 27 ga watan Oktoba, 2024 kan cewa su tattara kayansu su bara unguwannin birnin.
A ranar Litinin ne Wike ya soke takarda mallakar wasu filaye da aka bai wa kamfanin Julius Berger a Katampe da ke Abuja.
