Sarkin Hadejia ya jajenta wa Gwamnatin Jigawa bisa hatsarin tankar mai

Spread the love

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse

Majalissar Masarautar Hadejia ta kai ziyarar jajentawa gidan Gwamnatin Jihar Jigawa kan hatsrin tankar mai da ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 181 da kuma kwantar da wasu 81 a Asibiti da ke jinya a ciki da wajen jihar.

Galadiman Hadejia, Alhaji Usman Abduaziz shi ne ya wakilci Mai Martaba Sarkin Hadejia, Alhaji Adamu Abubakar Maje zuwa gidan gwamnatin domin miƙa sakon ta’aziyyar ga gwamnan jihar wanda mataimakinsa Alhaji Aminu Usman Gumel ya wakilce shi.

Galadiman ya ce labarin mutuwar da hatsarin ya tayar da hankalin Masarautar a lokacin da aka kai mutane asibitin Hadejia dom ƙoƙarin ceton rayukansu.

Ya kuma yaba wa mutanen yankin Hadejia masu kuɗi da ƴan kasuwa waɗanda suka yi ta bada gudunmawarsu wajen
ceton waɗanda abin ya shafa.

Tawagar Masarautar ta ƙunshi manyan Hakimau da ƴan Majalisar Sarki a yayin jajentawar.

Galadiman ya yaba wa gwamnatin jihar kan irin kulawar da ta ke bai wa marasa lafiyar da suke kwance a asibitoci bisa umarnin gwamnatin jihar.

Ya bayyana cewa, hatsarin ya jefa mutanen Hadejia cikin ruɗani da damuwa ganin yadda motoci suka yi ta wucewa da mutane a ƙone zuwa babban asibitin ƙaramar hukumar.

Da ya ke jawabi a madadin gwamnatin, Mataimakin gwamnan, Injiniya Aminu Usman Gumel ya ce yawan marasa lafiyar da waɗanda suka mutu ya ƙaru sakamakon wasuda aka same su a gonaki da wasu a gidajensu bayan sun kasa yi wa kansu magani inda suka fito aka kai su asibiti don ceto rayukansu.

By Babaji