
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Kano ta dakatar da wasu ƴan jarida 14 da ke aikin ruwaito labaran gidan gwamnatin jihar.
Kakakin gwamnan, Sanusi Bature ya bayyana hakan cikin wata takarda da ya fitar inda ya buƙaci ma’aikatun da lamarin ya shafa su turo wasu da za su maye gurbin waɗanda aka dakatar.
Saidai, bai bayyana dalilan da suka sabbaba ɗaukar matakin hakan da gwamnatin ta yi ba, amma wasu daga cikin ƴan jaridan da lamarin ya shafa sun ce sun samu rashin fahimtar juna ne da manajojin labarai na gwamnatin kan wasu damanmaki.
Sun kuma bayyana cewa, an dakatar da su daga ruwaito labarin zuwan Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, gaisuwar jajen hatsarin tankar mai a Jihar Jigawa a makon da ya gabata.
An kuma ruwaito cewa, ƴan jaridan sun fusata manajojin a lokacin da suka je suka gana da Gwamnan Jihar Bauchi a lokacin da ya kawo ziyara Kano yayin wani taron addini.
Jaridar ‘Premium Times’ ta ruwaito cewa ƴan jaridan da aka dakatar sun ƙunshi furodusoshi da masu ɗaukar hoto daga gidajen jaridun gwamnati da masu zaman kansu.
