Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin Tarayya ta janye ƙarar da ta shigar akan jami’in Binance

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnatin Nijeriya ta janye baki ɗaya tuhume-tuhumen da ta shigar akan wani babban jami’in kamfanin Binance Holdings mai suna Tigran Gambaryan, wanda aka tsare shi tun watan Afrilu kan almundahanar wasu ƙuɗaɗe.

Wani lauya da ke wakiltar Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati, EFCC kuma hukumar da ke bincike, ya sanar da janyewa daga ƙararrakin da ta shigar akan babban jami’in a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, a ranar Laraba, 23 ga watan Oktoba, 2024.

A lokacin da ya ke sanar da batun janyewar, lauyan ya ce Mista Gambaryan wanda ɗan ƙasar Amurka, jami’i ne na Binance Holdings kuma da ake bincikarsa kan ayyukansa na kamfanin.

Mark Mordi, wani babban lauya ne (SAN) da ke wakiltar Gambaryan wanda ya nuna amincewarsa da binciken, ya na mai cewa ma’aikacin baya ɗaya daga cikin waɗanda ke yin hukunci game lamuran da suka shafi kuɗin kamfanin.

By Babaji