Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur na Nijeriya (Na iskar gas), Ekperikpe Ekpo, ya ba wa kamfanin man fetur na ƙasa, NNPCL, da masu harkar iskar gas(LPG) umarnin dakatar da fitar da shi zuwa ƙasashen ƙetare daga 1 ga watan Nuwamba.
Mista Ekpo ya ba da wannan umarni ne a ranar Talata a yayin wani taron masu ruwa da tsaki a Abuja.
Wannan mataki na zuwa ne domin magance hauhawar farashin iskar gas da ‘yan Nijeriya suka fara fuskanta.
A cikin jawabin da mai magana da yawunsa ya yi, Louis Ibah, ya ce ministan ya nuna damuwarta game da yadda ake samun tashin farashin iskar gas ɗin a faɗin ƙasar nan.
“Muna kira ga kamfanin NNPCL da masu samar da isakar gas da su dakatar da fitarwa ko shigo da iskar gas Nijeriya daga 1 ga watan Nuwambar 2024 na ɗan wani lokaci,” in ji ministan.
Sannan ya ba da tabbacin cewa cikin kwanaki 90 hukumomin kula da albarkatun man fetur za su zauna da masu ruwa da tsaki domin fitar da farashin da ya kamata a sayar da iskar gas a Nijeriya wanda ya har da tsadar abin da za a kashe wajen samar da shi.
Ministan ya nuna akwai buƙatar tsayar da farashin iskar gas, domin bai kamata a riƙa ƙokarin sayar da shi a irin farashin da ake sayarwa a ƙasashe kamar su Amurka da ƙasashen Asiya ba, domin abu ne da ake yi a cikin gida.
“Game da tsari mai dogon zango kuwa, za mu fitar da wani tsari na samarwa da adana da kuma rarrabawa a cikin ƙasar nan cikin watanni 12 ba tare da an fitar da iskar gas ba ƙetare har zuwa lokacin da ya wadata kuma farashi ya tsaya sosai,” ministan ya ƙara fayyace matsayarsa.
Ya ce wannan dai mataki na tabbatar da an magance ƙalubalen da ‘yan Nijeriya ke fuskanta wajen samun iskar gas ɗin da sukan yi amfani da shi wajen girki.
Kuma sabon matakin da aka ɗauka zai tabbatar da wadatar da ba wa yan Nijeriya damar iya siya cikin sauƙi la’akari da matsalar tattalin arziki da ake fama da shi.
Tun a watan Nuwambar 2023 ne ministan ya kafa wani kwamiti mai ƙarfi da zai duba batun tashin farashin iskar gas wanda daraktan NMDPRA, Farouk Ahmed, ya jagoranta tare da sauran masu ruwa da tsaki a harkar samar da iskar gas ɗin.
Sai dai duk da ƙoƙarin ganin an kawo ƙarshen hauhawar farashin, iskar gas ya cigaba da tashin gwauron zabi a mabambantan lokuta inda ya kai har N1500 daga N1100 zuwa 1250 da ake sayar da shi a baya na kowanne kilogiram ɗaya.
