Kisan kiyashi ake yi a Gaza, ba yaƙi ba – Ofishin jakadancin Palestine

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Yayin da ake cigaba da tada zaune-tsaye tsakanin ƙasashen Gabas-ta-Tsakiya musamman a yankin Gaza na ƙasar Palestine inda a nan ne aka fi zubar da jinanen bayin Allah, lamarin ya yi ƙamari a Arewacin jihar inda aka fi ɗaiɗaita mutane da garuruwansu.

Wani abin takaicin shine yadda mutane ke ta mutuwa a kan titina saboda tsananin wahala ta yunwa da rashin matsuguni.

Cikin wata takarda da Jakadan Palestine a Nijeriya, Abdallah Abu Shawesh ya fitar, ya ce yayin da aka cika kwanaki 384, Amurka da Isra’ila na kisan kiyashi wa al’ummarsu, ya bayyana yadda adadin ke cigaba da hauhawa.

Adadin waɗanda suka mutu ya kai 42,603 wanda 17,000 daga ciki yara ne inda kuma aka samu jarirai 171.

786 daga ciki yara ne da ba su kai shekara ɗaya ba, 37 sun mutu saboda yunwa, da mata 11,673, sai ma’aikatan kiwon lafiya 1,047.

Sauran sun haɗa da; jami’an ‘Civil Defence’ guda 85 da kuma ƴan jaridu 177 da sauran su.

Bugu da ƙari, gawawwaki 520 ne aka gano a ƙaburburan asibitoci yayin da ba a ga mutane 10,000 ba.

Har’ilayau, sanarwar ta ƙara da cewa, akwai wasu dubunnai da ba a san halin da suke ciki ba a yankin West Bank.

Duk wannan danniya da wulaƙanci da al’ummar yankin ke fuskanta, an kai ga hana mutane fitowa su yi zanga-zangar lumana kan nuna ƙin amincewarsu ga irin kisan kiyashin da ake wa ƴan Palestine a ƙasashe da dama musamman na Arewacin Amurka da Turai.

By Babaji