
Daga RABI’U SANUSI
Wata babbar kotu mai lamba 15 dake Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Sunusi Ado Ma’aji ta bai wa hukumar zaɓe ta KANSIEC damar gudanar da zaben ƙananan hukumomi a gobe asabar.
Mai shari’a Sunusi Ado Ma’aji ya bayyana cewa Hukumar zaɓen Kano tana da damar gudanar da wannan zaɓen nata bisa yadda take da hurumi.
A ɓangarensa lauyan hukumar zaben ta KANSIEC da suka shigar da ƙara bisa yadda kotun tarayya dake Kano ta katange su da gudanar da zaɓen
Barr. Lurwan Umar (SAN) ya ce wannan hukunci ya yi daɗi na babbar kotun ta Kano.
Barr. Lurwan ya ƙara da cewa kamar yadda aka sani kusan Jihohi ashirin da wani an gudanar da zaɓe kuma tabbas a Kano ma za’a gudanar da zaɓen ta kamar yadda aka tsara.
Lauyan kan hukumar zaɓen ya kuma ce kotun ta buƙaci dukkan jami’an tsaron dake kowane ɓangare da su bada goyon baya tare da dukkan haɗin kan da ya dace wajen gudanar da zabe.
Shima daga ɓangaren daya daga cikin lauyoyin da aka shigar da ƙarar su wajen bada damar gudanar da zaben kuma lauyan Jam’iyyar APC, Barr.Nura Adamu yace su ba suna tsokaci bane kan kotu ta haramta zabe baki daya, ya ce abinda suke ƙorafi a nan shine suna ƙalubalantar waɗanda suke jagorancin hukumar ne da zasu kuma gudanar da zaɓen.
Idan za’a iya tunawa dai Gwamnatin Tarayya ta bada umarnin kowacce ƙaramar hukuma zata gudanar da zaɓenta dan a cigaba da tura masu hakkokinsu da za su yi wa al’ummarsu aiki kai tsaye.
