Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ribas na gudanar da bincike gadan-gadan kan ɓacewar Yahaya Faruk, wani mai yi wa ƙasa hidima (NYSC) da aka tura zuwa makarantar sakandaren gwamnati da ke garin Ikuru a jihar ta Ribas kuma ya ɓace tun ranar 14 ga Oktoba, 2024.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar ta Ribas, SP Grace lringe – Koko ya sanya wa hannu a ranar Laraba a Fatakwal ta ce, a ranar 15 ga Oktoba, 2024, shugaban makarantar Community Secondary School, Ikuru Town, Anderson Awaji Ogbana, ya kai wa rundunar rahoto, inda ya ce an rasa gano inda Faruk yake a cikin harabar makarantar ko kuma unguwar da ke kewaye.
Sanarwar ta ce, Faruk yana ɗan taɓa aiki a kamfanin haƙar ma’adinai na LDM, wanda kuma ke cikin garin Ikuru.
Bayan samun rahoton, ’yan sandan sun gayyaci Wen Hauiguo, manajan kamfanin haƙar ma’adinai na LDM, domin yi masa tambayoyi.
A ranar 16 ga Oktoba, an mayar da shi sashin binciken manyan laifuka (SCID) na jihar inda aka shjgar da ƙara a kansa kan ɓacewar Malam Faruk a matsayin ma’aikacin da ke aikin dare, daga ƙarfe 4:00 na yamma zuwa tsakar dare a kamfanin.
Sai dai sanarwar ta ruwaito, Wen na cewa bai san Faruk a matsayin ma’aikacin kamfanin ba, domin an ci gaba da gudanar da bincike tare da manajan rukunin Lai Ding Chi, wanda ya bayyana cewa a yammacin ranar 14 ga watan Oktoba, 2024, tsakanin ƙarfe 9:00 zuwa 10:00 na dare, wasu mutane biyu da ba a san ko su wane ne ba sun zo a kan babur, daga nan Faruk ya bar aikinsa ya raka su.
“A ranar 18 ga Oktoba, 2024, Kwamishinan ‘yan sandan da kansa ya yi hira da duk ɓangarorin da abin ya shafa. Rundunar ta yi amfani da hanyoyi da dama, ta yin amfani da fasahar zamani don gaggauta neman inda Faruk yake.
Bugu da ƙari, an umurci jami’an hukumar CID na jihar da su haɗa kai da kwamitin ci gaban al’umma (CDC) da sauran masu ruwa da tsaki a cikin garin Ikuru, da nufin ƙarfafa ƙoƙarin yankin na gano ɗan NYSC ɗin da ya ɓata,” inji sanarwar.
